Sanarwa Ofishin Ayatullahi Alawi Gorgany
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai
Wadanda mala’iku suka karbi rayukansu suna tsarkakakku suna masu cewa: “Aminci ya tabbata a gare ku, ku shiga Aljanna sakamakon abunda ku ke aikatawa.
'Yan Mintuna kadan a yau da kuma kwanaki bayan kokarin da tawagar likitocin masu kula da shi su ka yi ga wannan bawan Allah masoyi a zukatan al,umma kuma mai girma jagoran abun koyi na Shi'a, Ayatullahi Alawi Gorgany (Quddusa Sirruhush Sharif) ya daina motsawa inda rai yayi halinsa yana cike da soyayya, ga Ahlul Baiti ma'asumi masu tsarki (a.s) ruhinsa ya koma ga ubangiji.
Muna masu mika ta'aziyyar wannan rashi maras misaltuwa ga Sayyidina Baqiyatullah Al-Azam (Af), ga kuma halarar Jagoran juyin juya halin musulunci (Dm), Manyan malamai na makarantun hauza, al'ummar Iran masu daraja. da kuma masoya masu rike da jagorancin alu.umma a sassan duniya gaba daya, Za'a sanar tare da bayyana Lokacin jana'izar mai girma tare da binne shi daga baya.
Ofishin Ayatollah Alawy Gorgani (Rizwan Allah Alayh)
342/